Shugaban hukumar Zabe ta jihar Taraba Baba Yusuf ya sanar cewa hukumar ta tsayar da ranar 18 ga watan Agusta domin yin zaben cike gurbin wanda zai wakilci Takum 1 a majalisar dokokin jihar.
Yusuf ya sanar da haka ne ranar Laraba a Jalingo da yake ganawa da shugabanin jam’iyyun jihar.
” Bisa ga ikon da doka ta bamu ne ya sa na tsayar da ranar 18 ga watan Agusta domin cike gurbin wanda zai wakilci Takum 1.”
Idan ba a manta ba kujeran wakilin Takum1 ya zama fanko ne tun bayan rasuwar mai wakiltar karamar hukumar Hosea Ibi.
Dan majalisa Ibi ya rasu a watan Janairu 2018 bayan kashe shi da wasu suka yi garkuwa da shi inda bayan biyan su da akayi suka kashe.
Discussion about this post