FAAC ta saki naira biliyan 669

0

Kwamitin Raba Kudade na Tarayya, FAAC, ya saki naira biliyan 669 domin kasafta wa gwamatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

Kwamitin ya bayyana cewa an saki kudin ne domin gwamnatoci su iya biyan albashi domin rage radadin tsaikon biyan ma’aikatan gwamnati albashin watan Yuni da ba a yi ba a jihohi da yawa.

Zaman da aka yi cikin watan Yuni domin a kasafta kudi, bai haifar da ‘da mai ido ba, domin an yi ta tirka-tirka kan batun yadda za a raba naira biliyan 147 daga ribar man fetur da NNPC ke bayarwa.

Tun bayan wannan lokaci, sun sake zama har sau biyu, amma aka kasa cimma matsayar abin da za a raba, wanda haka ya kawo aka daga taron har sai yadda hali ya yi.

Da yawan ma’aikatan gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi basu karbi albashin watan Yuni ba.

Maimakon a yi ta zaman dirshan a haka, sai gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yin amfani da kudaden ribar watan Mayu 2018 da za a raba, ta sake su domin a biyan albashin watan Yuni da su.

Sanarwar da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Kudade, Hassan Dodo ya aiko wa PREMUM TIMES a ranar Juma’a, ta bayyana yadda aka rarraba kudaden.

“Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 282.2, gwamnatocin jihohi sun tashi da naira bilyan 181.7 yayin da kuma aka raba wa kananan hukumomi naira 136.5

Share.

game da Author