‘Yan bindiga sun kashe wani ma’aikacin CBN a Gusau

0

Wasu da ba asan ko su waye ba sun kashe wani ma’aikacin babban bankin Najeriya CBN a garin Gusau.

Kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu ya tabbatar da aukuwar wannan mummnunar abu.

” Wadannan ‘yan bindiga sun far wa gidan Kabiru Zango da karfe uku da rabi na dare inda suka dirka masa harsashi a tsakiyar kansa.

Kafin ‘yan sanda su iso wannan wuri bayan waya da akayi musu wadannan mutane su gudu, saidai ya ce tuni ‘yan sanda sun fara bincike a kai.

Tuni dai har an tafi da gawar Zango Katsina da nan ne asalin jihar sa don yi masa sutura.

Share.

game da Author