Dalilin da ya sa na bayyana ra’ayin sake yin takara da wuri – Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya sa ya fadi wa ‘yan Najeriya da duk duniya ra’ayin sa na sake yin takara a 2019 shine don a sami daidaituwa a Jam’iyyar su ta APC.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne da yake zantawa da kungiyar gamayyar kungiyoyi masu yi masa kamfen wanda shugaban ta Umaru Dembo ya ke jagoranta.

” Ya zama min dole in sanar wa uwar Jam’iyyar mu cewa ina so in yi takara a 2019 da wuri saboda a dan samu natsuwa da kwantar wa wasu da dama da hankula.

” Sannan kuma hakan ya sa an sake yin zabubbukan wakilai da shugabannin jam’iyyar mu ta APC tun daga kasa har sama.

” Idan kun tuna a da wasu shafaffu da mai ne suka zama a wuri daya su rubuta sakamakon zabe a kasar nan sai Allah ya taimaki Najeriya aka kawo na’urar mai tantance wanda ya kada kuri’a. Wannan damar da aka samu yasa an sami nasara sannan aka ba mutane wadanda suka zaba a 2015.

Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su zabi wadanda suka ga sun dace, wadanda zasu yi alfahari da su.

A nashi tsokacin, Dembo ya ce wannan gamayyar kungiyoyi zasu dukufa ne wajen sake tallata shugaba Buhari a kasar nan , sako-sako, lungu-lungu, kurdi-kurdi, Kwararo-Kwararo domin ganin ya lashe zaben 2019.

Share.

game da Author