Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sa ranar da za ta gudanar da zabukan cike-gurbi har guda hudu da ke a gaban ta.
Hukumar a jiya 19 Ga Yuli, ta bada sanarwar cewa za ta gudanar da zabukan cike gurabu hudu a ranar 11 Ga Agusta.
Zabukan da za a gudanar a ranar sun hada da Sanatan Katsina ta Arewa mai wakiltar Shiyyar Daura, mazabar Shugaba Muhammadu Buhari, na Bauchi ta Kudu da kuma Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Lokoja/Kogi da Koton Karfe daga jihar Kogi, sai kuma dan majalisar jiha daga mazabar Obudu ta cikin jihar Cross River.
INEC ta yanke wannan matsaya ce bayan da Majalisar Tarayya ta sanar da su a rubuce cewa wadannan gurabu ba su da mai wakilci a halin yanzu.
Dama haka ya ke a kan ka’ida, duk wakilin da aka tsige ko ya rasu, Majalisa za ta sanar wa INEC, ita kuma sai ta aza ranar da za ta gudanar da zaben cike gurbi.
Sakataren Hukumar Augusta Ogakwu, ya bayar da wa’adin ranar 25 Ga Yuli cewa kowace jam’iyya ta gunadar da zaben fidda-gwani, yayin da kowane dan takara zai maida fam din sa mai lamba CF001 da CF002 a ofishin INEC zuwa ranar 27 ga Yuli.
Har ila yau, ya ce kada kowace jam’iyya ko dan takara ya wuce ranar 3 Ga Agusta bai kai sunayen ejan-ejan din sa ba a ofishin INEC.
A karshe INEC ta ce daga ranar 9 Ga Agusta, kada wani dan takara ya sake ya yi kamfen.