Mutane uku sun mutu, yayin da wasu da dama suka ji ciwo a lokacin da wani jirgin kasa ya banke wata mota kirar bas a daidai Pen Cinema a Legas, yau Juma’a.
Wani da aka yi hadarin kan idon sa mai suna Raji Oladimeji, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN cewa hadarin ya faru a daidai lokacin da direban bas din ke kokarin yin kwana a kan titin jirgin kasan.
“Sai da muka gargadin direban bas din muka ce kada ya kuskura ya tsaya yin kwana a kan titin jirgin, saboda ya kusa da wuri, amma ya ki jin maganar mu.
“Jirgin na isowa ya bangaji bas din, sai fasinjoji uku daga cikin wadanda ke makale da jirgin a waje, suka fado kasa, suka mutu, wasu kuma da suka fado suka ji raunuka.” Inji Oladimeji, wani mai gyaran lantarki.
Ya ce wasu hasalallun matasa sun banka wa bas din wuta, yayin da aka dauki wadanda suka ji ciwo aka garzaya da su asibiti.
Manajan Tashar Jirgin Kasa ta Lagos, Jerry Oche ya ce ya tabbatar da cewa hadarin ya auku ne da misalign karfe 9:30 na safe.