An sake daga shari’ar El-zakzaky

0

Kotu da ke shari’ar karar da gwamnatin Kaduna ta shigar kan shugaban kungiyar Shi’ite, Ibrahim El-zakzaky a Kaduna ta sake daga shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Agusta.

Alkalin kotun Gideon Kurada ya bayyana cewa kotu ta yi haka ne don a samu damar mika wa wasu da ke cikin jerin wadan da ake tuhuma a karar takardun sammaci.

A dalilin wannan shari’a ta yau kusan babu wani aiki da akayi a jihar Kaduna.

Bankuna da ofisoshi basu bude wuraren aiki ba a yau Laraba sai da yamma.

Share.

game da Author