Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta bayyana cewa a ranar Asabar da safe za ta janye dukkan jami’an tsaron da ke gadin manyan shugabannin siyasa a jihar Ekiti.
Mataimakin Shugaban ‘Yan sanda na Kasa, Habila Joshak ne ya furta haka yau a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
Ya ce janye jami’an tsaron zai kawo ingancin zabe a ranar.
Ya kara da cewa tuni sun sanar wa Gwamna Ayodele Fayose da dan takarar gwamna Kayode Fayemi cewa za su janye musu jami’an tsaron da ke gadin su, da sanyin safiyar Asabar kafin a fara zabe.
“Ba za mu bar duk wani mai fada-a-ji ya je wurin akwatin jefa kuri’a tare da jami’an tsaro ko da ‘yan dab aba. Saboda yin haka karya dokar zabe ce.”
Joshak ya gargadi ‘yan sanda da cewa duk wanda ya kuskura ya yi wa wani dan siyasa ko mai mulki aiki a ranar zaben gwamna a Ekiti, to ya kuka da kan sa.
” Duk wanda ya kuskura ya fito da kudi ya sayi kuri’u a wurin zabe, to ya sai wa kan sa alakakai.”
“Idan ka jefa kuri’a, za ka iya komawa can nesa ka tsaya ka na jiran a yi kidaya, domin ka kare kuri’ar ka, ‘yancin ka. Wannan ba mu haka ba. Amma idan ka saci akwatu, za mu guntule mana hannu nan take.
“Idan kuma ka saci akwatu ka nemi shekawa a guje, za mu ragargaza maka kafafu kawai.”
“Idan ka yi shigar-burtu ka yi bad-da-kama da shigar mutum-mutumi (masquarade), za mu damke ka, mu farke wannan rigar tsumman mutum-mutumin banzan da ka yafa kowa ya gan ka.”