TA LEKO TA KOMA: Croatia ta doke Ingila da ci 2-1

0

Bayan gumurzu da akayi ta kusan awowi uku kasar Croatia ta jefa kwallon ta ta biyu a ragar kasar Ingila.

Mario Manzukic ne ya jefa kwallon bayan an dawo hutun rabin lokaci na karin lokaci da aka yi.

Yanzu dai Kasar Ingila za ta kara ne da kasar Belgium don neman gamawa a na uku.

Ita kuwa kasar Croatia za ta gwabza ne da kasar Faransa.

Za a buga wasar karshe ne ranar Lahadi mai zuwa, sai dai kafin nan za a buga wasan Ingila da Belgium ne ranar Asabar.

Share.

game da Author