Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan jajircewa da yayi in da ya garzaya har kotun koli domin abi masa hakkin sa kuma yayi nasara a kai.
Buhari ya bayyana cewa irin wannan hukunci ne yayi ta nemar ayi masa irinta a lokutta uku da ya yi ta kai karar murdiyya da akayi ta masa da yi takarar shugabancin kasa Najeriya.
Ya ce samun yi masa adalci da akayi abin a taya sa murna ne.
Saraki dai ya doke gwamnatin tarayya ne bayan ta daukaka kara cewa wanke shi da kotun daukaka kara tayi ba ta amince da hukuncin ba.
Nan da nan Saraki bai yi wata-wata ba ya nausa kotun koli domin a bi masa hakkin sa na cewa bai karya dokar kasa a kadarorin sa da ya bayyana.
Garba Shehu ne ya saka wa sakon shugaba Buhari hannu.