INEC za ta dakatar da yin rajista a ranar 17 Ga Agusta

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta bayyana cewa za ta dakatar da ci gaba da aikin yin rajista a ranar 17 Ga Agusta, har sai bayan zaben 2019.

Hukumar ce ta yi wannan sanarwar a cikin wata takardar manema labarai da Kwamishinan Zabe Kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kai masu yin Rajista, a Abuja.

Solomon Soyebi, ya ce za a ci gaba da aikin karba da bayar da katin zabe har sai ana saura mako daya kacal kafin zabe, ranar 12 Ga Fabrairu, 2019.

Shugaban ya ce an dauki wannan mataki ne bayan da Hukumar ta tuntubi manyan masu ruwa da tsaki a harkar zabe na fadin kasar nan.

A cikin satin nan dai INEC ta yi taron ganawa da shugabannin jam’iyya, kafafen yada labarai, kungiyoyin sa-kai da jami’an hukumomin tsaro.

Ya ce dukkan masu ruwa da tsaki sun amince a samu wadatacciyar ratar lokaci daga ranar da aka daina yin rajista zuwa lokacin zabe, ta yadda za a samu lokacin daukar bayanai da, tattarawa da killace na duk wanda yayi rajista a kwamfuta zuwa ranar da za a fitar masa da katin zabe.

Soyebi ya karkare da cewa INEC zai zaburar da bangaren yada labaran sa ta yadda za a tabbatar da cewa duk wani dan Najeriya da ke son yin rajista, ya samu ya karbi katin rajistar sa kafin mako daya a fara zabe.

A karshe kwamishinan ya roki daukacin ‘yan Najeriya su hada kai a samu sahihin zabe kamar yadda INEC ta yi alkawari a jihar Osun da Ekiti da kuma zaben 2019 na kasa baki daya da aka maida hankali a kan sa.

Share.

game da Author