Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya soki kashe jami’in dan sanda da mabiya akidar Shi’a suka yi a garin Kaduna da kakkausar murya ya na mai cewa tabbas za su fuskanci fushin gwamnati.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne daruruwan mabiya akidar Shi’ a suka fito tinunan garin Kaduna domin yin zanga zangar ci gaba da kira ga gwamnati da ta saki shugaban su Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
Mabiyan sun fito titunan ne a daidai za a ci gaba da shari’ar shugaban su a kotu dake Kaduna.
Duk da cewa hakan bai yiwu ba, bayan an dage ci gaba da zaman shari’ar, hasalallun matasa suka far wa jama’a dake gudanar da hidimomin su a tsakiyar cikin garin Kaduna, wato Ahmadu Bello way.
Sun farfasa motocin masu haya, sannan suka far wa wani dan sanda babu gaira babu dalili.
Duk da cewa dan sandan ya nemi ya gudu don ya tsira da ransa, matasan suka make shi inda ya yanke jiki ya fadi.

Daga nan ko suka far masa da duka, jifa har ya ce ga duniyar ku nan.
Sannan suka yi ragaraga da moton fatorol din da yake tukawa.
Gwamna El-Rufai ya ce gwamnati ba zata zuba ido ta bari haramtacciyar kingiya na yin abin da ta ga dama a jihar ba.
Ya ce tabbas za a abi silar abin kuma duk wanda a ka kama za a hukunta shi kamar yadda doka ta shar’anta.
Daga nan sai ya kara da cewa kamar yadda gwamnati ta yi alkawarin kare lafiya da dukiyoyin mutane ba za a bari wasu tsiraru sannan haramtattun kungiya ba su nemi tada zaune tsaye a kasar nan.
Discussion about this post