Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ko da bai sami tikitin zama dan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP ba zai yi wa jam’iyyar aiki tukuru don ganin ta sami nasara a zabukan dake tafe.
Atiku ya fadi haka ne a ziyarar bayyana ra’ayin sa na fitowa takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar a zabe mai zuwa da ya kai hedikwatar jam’iyyar a Abuja.
Atiku yayi kira ga shugaban jam’iyyar Uche Secondus da a tabbata an yi zaben fidda dan takara da zai karbu wajen ya’yan jam’iyyar.
Ya bada misali da zaben fidda dan takarar gwamna da akayi a jihar Ekiti, yana mai cewa yadda akayi zaben ya bada sha’awa matuka.
Daga nan yayi kira ga jam’iyyar da suyi koyi da hakan.
Shugaban PDP, Secondus, ya tabbatar wa Atiku cewa yanzu jam’iyyar ba kamar da bace. Za a yi zabe ne wanda kowa zai amince da ita.
Yanzu dai akwai kwararrun ‘yan takara uku kenan da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma Atiku Abubakar.