GANGAMIN APC: Buhari ya sulale daga filin taro; A wasu rumfunar kuwa dambacewa aka yi

0

Jim kadan bayan kada kuri’un su a zaben sabben wadanda za su rike ragamar jam’iyyar APC na tsawon shekaru hudu masu zuwa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo, shugaban Majalisar Dattawa da na wakilai Bukola Saraki da Yakubu Dogara duk sun fice daga filin taron zaben.

Masu yin fashin baki kan harkar siyasa sun ce wannan gangami bai yi armashi ba, bai yi kama da gangamin tarin siyasa da aka saba gani ba.

A wasu rumfunan jihohi kamar su Delta kuwa an ba hammata iska ne inda aka tarwatsa wannan rumfa sannan aka kakkarya kujerun zaman da aka tanada wa wannan rumfa.

Sanata Dino Melaye dake wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar Dattawa ya yi wa taron gwalo cewa wannan gangami taron wasan kwaikwayo ne kawai amma ba irin na jam’iyya mai mulki ba.

Share.

game da Author