RASHA 2018: Akwai fargabar kai wa gidajen kallon kwallo hari-Jami’an tsaro

0

Jami’an tsaron kasar nan da suka hada da ‘yan sanda da kuma jami’an shigi da fice na kasa, sun yi gargadi da cewa akwai famamun za a kaswa gidajen kallon kwallo hare-hare a yayin da ake gudanar da gasar cin ko fin duniya.

Sun ce duk da cewa jami’an tsaron kasar nan, sun sa ido sosai, to ya na da kyau jama’a musamman matasan kasar nan a iyar tsawon kwanakin da za yi n gasar a Rasha.

An dai fara gasar ranar 15 Ga Yuni, za a rufe ranar 15 Ga Yuli.

A c ikin wasikar da rundunar ‘yan sanda ta aiko wa PREMIUM TIMES, ta yi kira ga kwamishinnin ‘yan sandan jihohin kasar nan da su kara maida hanukulan su wajen tsananta sintiri a yankunan su.

Ita ma hukumar shige da fice ta kasa ta umarci jami’an ta da su tsananta sa-ido wajen tabbatar da ceewa ba a taba musu kayyakin su ba.

Idan ba a manta ba, an kai hari a garin Damaturu, a lokacin da ake kallon wasan gasar cin kwallon duniya na shearar 2014, inda aka kashe ‘yan kallo 21.

Share.

game da Author