Wasu shugabannin jami’o’i ‘yan harkalla ne – Ministan Ilimi

0

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa wasu shugabannin jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare, ‘yan harkalla ne.

Adamu ya yi wannan bayanin ne a yayin da ya ke jawabi a taron duba fasalin tsare-tsaren hukumar shirya jarabawa ta JAMB na shekarar 2018, da ya gudana a Gbongan, jihar Osun a jiya Talata.

“Wasun su su na gudanar da aikin su a kan turba da tsari na rashin gaskiya. Sannan kuma sun san cewa idan da binciken su za a yi, to bai cancanta su na kan mukamin ba. Saboda ba su da gaskiya, ‘yan harkalla ne.

“Mu na da kwakwaran shaidu da ke tabbatar da wasu daga cikin harkallar da wasun ku ke aikatawa, da ta hada da daukar dalibai ba bisa ka’ida ba, karin kudin fam ga dalibai masu neman shiga jami’a da kuma kin bin ka’idar wasu ayyuka da suke gudanarwa.”

Daga nan ya ce duk wanda aka kara kamawa, to ya kuka da kan sa.

Ya kuma kara yin gargadin cewa daga yau kada wata jami’a ta kara sayar da fam na jarabawar shiga jami’a ta Post-UME sama da naira 2000.

Share.

game da Author