Dan wasan Najeriya Ahmed Musa ya zura wa kasar Iceland kwallaye biyu, wadanda masu kallon kwallo ke kira da suna cin-Allah-tsine-uwar-mai-karya, kwallayen da suka kankare wa Najeriya dusashewar da martabar ta ta yi a wasan Gasar Cin Kofin Duniya da ake fafatawa a Rasha.
Bajintar da Musa ya yi ta jefa kwallaye biyu, ta ruda Najeriya, inda gaba daya birane da kauyuka aka barke da ihu da murnar da kade-kade da bushe-bushe.
Ahmed Musa ya tura wa Iceland haushi, ya bakanta ran kasar Argentina, kuma ya harzuka ran dan wasa Leonel Messi, wanda a yanzu kuma shi duniya ta sa ido a gani ko zai yi bajintar sa ta karshe a gasar cin kofin duniya, ko kuwa zuwan-kare-karofi zai yi wa Rasha.
Idan Najeriya ta yi galaba a kan Argentina, to ta karya duk wani lagon tarihin wasan cin kofin duniya da Messi ya kafa, domin gida ‘yan wasan Argentina za su koma dauke da buhun kunya.
Sai dai kuma tuni rahotanni sun nuna cewa Argentina ta karaya, domin ‘yan wasan da mai horaswa sun fito a kafafen watsa labarai suna yamadidi da juna, har su na kiran a kore shi kawai.
Shi ma mai horaswar ya shiga jaridu ya na bayyana cewa ‘yan wasan Argentina duk ta-gina-ba-ta-shiga ba ce, rashin kokarin su ya sa Messi ya kasa tabuka komai, domin karfe daya inji, ai ba ya yin amo.
Kwallon da Victor Moses ya shanfamo a cikin yadi na 18 a gidan Iceland, wadda dan wasa Ahmed Musa ya café da kafar dama, sannan ya antaya ta a cikin raga, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, ta tayar da kaimin duk wani mai kallon wasa a Nijeriya aka barke da ihu da karaji.
Ita ce kwallo ta farko da Najeriya ta ci a wannan gasa, sannan kuma gwanitta da kwarewar da Musa nuna wajen tare kwallon da doka ta, ya burge hatta wadanda ba su ganin kan sa da gashi.
Kwallo ta biyu da ya jefa kuwa, baya ga burge daukacin ‘yan Najeriya da ya yi, za ta zama abar tozartawa ga kasar Iceland, wadda a wasanta na cin kofin duniya 16 a jere, wannan ne karo na farko da aka yi nasara kan ta.
Baya ga firgita Iceland da Musa ya yi, kwallayen da ya ci zai sa ‘yan wasan Argentina kwana a gaban talbijin su na tariyar kallon yadda ya wulakanta Iceland, a lokaci daya kuma su rika tunanin yadda za su kaya su kwaranyecda Najariya, a wasan Argentina na ko a ci ko a mutu da za ta yi da Najeriya.
Masu sharhin kwallo da dama a yau sun tabbatar da cewa idan ‘yan wasan Najeriya suka nuna irin kaimi, bajinta, kwarewa da natsuwa da yawan kai farmaki kan Argentina, kamar yadda suka yi a wasan su na yau da Iceland, to za su kunyata Messi da rundunar sa.
A yau dai magoya bayan Najeriya a katafaren filin kwallon birnin Volgogard Arena da ke Rasha, sun barje gumen su, sun share kuma sun katalle.
Daga cikin ‘yan kallo a filin kuwa har da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, wanda wasu ke ganin cewa mai yiwuwa ma shi ne ya kara wa ‘yan wasan Najeriya kwarin-guiwar da ta sa suka yi namijin kokarin da suka fitar da Najeriya kunya.
Da farko an dauka Najeriya ba za ta yi wata rawar gani ba, domin har aka tafi hutun rabin lokaci, babu wani dan wasan Najeriya da ya buga kwallon da ya tada hankalin mai tsaron gidan Iceland.
Sai dai kuma labari ya sha bamban, inda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, aka rika zabga wa Iceland ruwan kibau din hare-hare.
Ko kafin Ahmed Musa ya ci kwallo ta biyu, sai da ya kusa cin wata kwallo, inda ta bugi karfe, kadan ya rage ta fada cikin ragar Iceland, da kwallaye uku ya ci kenan.
Ganin yadda Ahmed Musa ya yi bajinta a yau, mai horas da ‘yan wasan Najeriya ba zai sake yin gangancin ajiye shi a benci ba, ko da kuwa giyar wake ya sha, kamar yadda ya ajiye shi a wasan Najeriya da Croatia.