Za a fara sarrafa maganin cutar sikila a Najeriya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta fara sarrafa maganin cutar sikila mai suna ‘Niprisan’ a kasar nan.

Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta amince wa kamfanin sarrafa magunguna ‘May and Baker’da ma’aikatar binciken magunguna na kasa (NIPRD) don sarrafa wannan magani.

Ya ce wakilan ‘May and Baker’ da NIPRD ne suka saka hannu a takardan yarjejeniyyar sarrafa wannan maganin da gwamnati ta bada izinin haka.

Adewole ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne domin kawar da cutar daga kasar nan kwata-kwata.

Share.

game da Author