Wani hasalallen Sanata da aka bata wa rai a cikin jam’iyyar APC, ya bayyana cewa idan APC ta zabi Adams Oshimhole a matsayin shugaban ta a zaben da jam’iyyar za ta gudanar yau, a taron gangamin ta Abuja, to zai iya ceto APC daga tarwatsewa.
A fili ta ke cewa dai Oshimhole ne zai kasance shugaban jam’iyya, ganin yadda a jajibirin zabe duk sauran ‘yan takara uku suka janye, aka bar shi shi kadai babu abokin hamayya.
A wata takardar da Sanatan ya turo wa PREMIUM TIMES a yau, ya bayyana APC a matsayin wata “solobiyon tsintsiyar da ko cikin daki ba ta iya sharewa, balle ta share dattin cikin kasa baki daya.”
“A cikin shekara uku da APC ta yi ta na mulki, ba ta tsinana komai a jam’iyyance ba, sai raba kawunan ‘yan jam’iyya da kuma sai kuma ita kanta ta zama datti, bola da kuma shaddar zubar da dagwalon kazanta.”
“Oyegun zai tafi ya bar jam’iyyar APC a matsayin ta na jam’iyyar da ta gudanar da zaben shugabannin jiha na coge, jabu, boge mai cike da rashin adalci da darkalla da kuma zambar al’umma, kuma haramtacce.”