Masu garkuwa sun sace mutane 23 a hanyar Birnin Gwari da safiyar Juma’a

0

Muhammed Kebi, ya bayyana wa Jaridar PRNigeria cewa Allah ne ya tsirar dashi da safiyar Juma’a bayan arangamar da suka yi da masu garkuwa a Kwanar-tsauni tsakanin Udawa da Labi” a titin Birnin-Gwari.

Kebi ya ce masu garkuwan sun tare hanyar ne inda suka tare motoci biyar sannan suka tattara mutane har 23 suka auna da su cikin daji.

Cikin wadanda aka sace akwai mata mai goyo da dan karamin yaro.

Sai dai har yanzu babu wani bayani game da hakan daga jami’an tsaro.

Share.

game da Author