Mahara dauke da makamai sun far wa wasu kauyuka har 10 a jihar Zamfara inda suka sace shanu da dukiyoyin mutane.
Kauyukan da suka fada cikin wannan ibtila’I sun hada da Fura Girke, Majira, Kanawa, Yargeba, Takoka, Bargaja, Bundungel, Bantsa, Unguwar Matanda Makera.
Maharan sun sace shanu iya san ransu da wasu dabbobin da dama sannan sun tafi da wani mutum daya.
Mazauna wadannan kauyuka kuwa basu ga ta zama ba domin kusan dukkan su arce wa cikin dauji suka yi suka bar wa barayin garuruwan su.
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala ya nuna juyayin sa ga mutanen wannan kauye sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo wa mutanen jihar dauki.
” Wannan masifa ya ishe mu hakanan, muna rokon gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo mana dauki domin abin ya wuce gona da iri.
Sannan kuma ya yi kira ga jami’an tsaron dake aiki a jihar da su tsaurara matakan tsaro a jihar.