Buhari na shirya mini makirar kutunguila don aci mutunci na a kasar nan – Obasanjo

0

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koka kan wasu bayannan sirri da ya iske sa kan shirin da gwamnatin Buhari ke yi na ganin an wulakanta shi ko ta halin kaka.

Obasanjo ya bayyana haka ne a wata takarda da kakakin tsohon shugaban kasar Kehinde Akinyemi ya saka wa hannu.

Ya ce tun bayan wasikar da ya rubuta wa Buhari a watan Janairu kan yadda yake tafiyar da ayyukan gwamnatin sa a kasar nan, Buhari ya sama kasa karan tsana. Ya fara shirya masa makininita da kulle-kulle kawai domin aga bayan sa.

Obasanjo ya ce ba zai yi shiru ya rufe baki ba ya bari mutanen kasa na wahala saboda rashin iya mulki da gwamnati mai ci ke yi a kasar nan.

” Ina so kusani cewa duk naji irin makircin da ake shiryawa a kai na. Na farko dai ana so a kirkiro wasu labaran karerayi da takardun kage domin a samu dalilan da za a iya kama ni ko kuma a hada ni da hukumar EFCC.

” Sannan kuma duk da haka ana neman hanyar da za abi a binciki zamanin mulki na domin a samu dalilin ci mini mutunci.

” Bayan haka kuma na ji daga sahihiyar majiya cewa an sa suna na a jerin sunayen da jami’an tsaro suka sa wa Ido a kasar nan. Sannan kuma munji labarin cewa ana so a kwace masa Fasfo din sa kuma a kange shi wuri daya duk don kada ya sake cewa komai.

” Abin kunya ne yadda gwamnati ta karkata zuwa ga yin farautar yan adawa kawai, da duk wanda ya ke adawa da ita. Ta sani cewa komai yayi farko, yana da karshe.

Kehinde Akinyemi ya ce duk da wadannan sakale-sakale da gwamnatin Buhari ke kokarin yi wa Obasanjo ba zai hana shi ci gaba da fadin gaskiya ba don a gyara.

Share.

game da Author