Shugaban Hukumar Kula da Hannayen Jarin Kamfanoni (SEC), Munnir Gwarzo, ya kalubalanci dakatarwar da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi masa.
Gwarzo ya maka ministar kotu, tare da Hukumar ta SEC da kuma Antoni Janar na Tarayya, inda ya kalubalanci dakatarwa da aka yi masa.
Ya kai karar ce a Kotun Hukunta Laifukan Kamfanoni da Masana’antu, a jiya Litinin da ke Abuja.
Gwarzo, wanda aka dakatar tun cikin watan Nuwamba, 2017, a bisa zargin sa da danne wasu kudade da ya ce bai san da zance ba, ya nemi kotu da ta tantance wasu sarkakkun bayanai domin a fitar da tsakuwa daga cikin tsaki.
Na farko ya na so kotu ta yi bayanin shin ko Minista na da karfin ikon dakatar da shi? Tunda shi da Shugaban Kasa ne ya nada shi ba it aba.
Ya na so kuma ya sani shin ko dokar da Kemi ta yi amfani da ita har ta dakatar da shi, za a iya amfani da ita kan Darakta Janar na Hukumar SEC.
Sannan kuma Gwarzo na son kotu ta tantance shin ko kwamitin binciken da Minista ta kafa masa bai nuna son kai wajen binciken sa ba.
Lauyan Gwarzo, Abdulkarim Mustapha (SAN) ya kara da cewa su na neman kotu ta yi watsi da rahoton da kwamitin binciken Gwarzo ya fitar.
Sannan ya na neman a maida shi kan mukamin sa, tare da biyan sa dukkan albashi da alawus din da na tsawon wtannin da ya shafe a dakace.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, hukumar ICPC ita ma ta gurfanar da shi in da take tuhumar sa da laifin yin almundahana da kudaden hukumar SEC din.
Ana zargi Munnir da biyan kan sa kudade da ya kai naira miliyan 114 ba tare da ya bi yadda doka ta shimfida ba.
Munnir bai amsa laifi ba, daga nan sai Alkali Hussein Baba-Yusuf ya bada belin sa kan miliyan 25.