Majalisar Koli ta Musulunci ta kwada wa ‘yan jarida guduma a kai

0

Babban Sakataren Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Ishaq Oloyede, ya caccaki ‘yan jarida da shugabannin addinai inda ya zarge su da rura wutar rudani da kuma nuna bangaranci da addinanci a kasar nan.

Oloyede, ya yi wannan caccakar ne a wurin taron lacca da aka shirya na Kamfanin Gidan Jaridar The Point, a jiya Litinin a Legas.

Oloyede wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar JAMB ta shiga jami’a, ya ce ba abin mamaki ba ne idan aka ga ‘yan siyasa na kitsa karairayi tare da danne gaskiya domin haddasa rudu da rabuwar kawuna a kasa.

Ya ce amma ba zai taba yiwuwa a zura ido a kyale baragurbin shugabannin addinai da kuma ‘yan jaridar da aka san sun amsa sunan su wajen kwarewar aiki su kai kasar nan su baro ta hanyar yada farfaganda da karairayi cikin al’umma ba.

“Duk mai irin wannan mummunan halin ba zai gama da duniya lafiya ba. Idan ma ya gama lafiya, to ya je lahira ya iske mummunan sakamakon hisabin san a jiran sa.” Inji shi.

Da ya ke magana a kan rikicin Fulani da Tivi yace dadadden rikici ne, wanda a baya ma tarihi ya nuna cewa akwai kwakwaran zumunci a tsakanin Fulani da Tivi.

SHUGABANNIN KIRISTOCIN KASAR NAN

Ya kuma tunatar da cewa a baya lokacin mulkin Obasanjo an yi mummunan rikicin Fulani da Tivi amma ‘yan jarida ba su maida abin fadan addini ba, sai yanzu da Buhari ke kan mulki suka maida rikicin na addini.

Ya ce a wancan rikicin, Obasanjo ne shugaba, Mike Okiro ne Sufeto Janar na ‘yan sanda, yayin da TY Danjuma ne Ministan Tsaro. Amma ‘yan jarida ba su ce ana kashe Fulani a gwamnatin da kiristoci suka yi wa mulki kaka-gida ba.

Ya kuma yi kaca-kaca da wasu shugabannin addinin Kirista masu yawan sanya rigar addini a dukkan al’amurran da suka shafi kasar nan domin su goga wa musulmi da kuma musulmin shugaban kasa kashin kaji.

Da ya tabo batun kashe-kashe kuwa, ya ce an fi kashe musulmai da yawa a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, amma shugabannin musulmi ba su taba cewa Jonathan ne ke kashe su ba.

Ya ce duk da surutan da aka rika yadawa cewa da gangan Jonathan ya bari Boko Haram ta kassara Arewa, wannan bai sa Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta fito ta dora masa laifi ba.

Ya ce amma yansu wasu ‘yan-ta-kifen shugabannin addinin Kirastanci sun fito su na dora wa Buhari laifi.

“Me ya sa mu lokacin da kiristocin kudu maso kudu suka rika kashe musulmai ba mu ce laifin Jonathan ba ne?”

Don haka ya ce babu manyan shaidanun shugabannin addinai kamar wadanda ke cewa Buhari ne ya daure wa Fulani makiyaya gindi su na kashe-kashe.

BABU SAURAN MASALLACI A TAFAWA BALEWA, AN DAINA KIRAN SALLAH A GARIN

Shugaban na Hukumar JAMB ya kuma koma kan yadda ‘yan jarida ba su yayata rashinn adalcin da ake yi wa musulman kasar nan, sai su danne ba mai ji balle har wani ya gani ko ya sani.

Oloyede ya ce “Ku dubi garin Shugaban Najeriya na farko, wato Tafawa Balewa. A yau babu musulmai a garin, duk an kore su, sun yi gudun hijira. Bubu sauran masallaci ko daya kuma an ma daina kiran sallah a garin. A jihar Bauchi fa.”

“Bayan an yi wa Musulmai kisan kiyashi a garin an kori wadanda suka rage sun gudu an yi ta kai gwaro ana kai mari wurin Jonathan domin musulman Tafawa Balewa su koma garin su na asalin gadon-gadon, amma abin ya ci tura.

“Har yanzu a zamanin mulkin Buhari ma shugabannin addinin musulunci sun yi ta kokarin a maida musulman Tafawa Balewa gida, amma hakan bai kai ga samun nasara ba. Nan a jihar Bauchi ba wani wuri mai nisa ba.”

Daga karshe sai ya yi kira ga kwararrun ‘yan jarida masu bin diddigi da binciken bayanai su maida hankalin su kan matsalar da musulmin Tafawa Balewa ke ciki.

Share.

game da Author