Fayemi ya tsallake rijiya da baya

0

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, kuma dan takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi ya tsallake rijiya da baya, bayan kuskure wa harbin bingida da wani dauke da bindiga ya nemi ya kashe shi.

Shi dai Fayemi ya isa garin Ado Ekiti ne tare da gwamnan jihar Ondo daga Akure domin halartar taron jam’iyyar don ci gaba da shirye shiryen zaben gwamnan jihar da ya kunno kai.

Shigar sa dakin taro ke da wuya sai ko wani ya tashi a cikin dakin taron ya zaro bindiga daga aljihunsa ya saki harsashi zuwa gare sa.

Allah ya sa bindigar bata sami shi bs sai dai ta sami wani tsohon dan majalisae tarayya da ke kusa da shi.

Tuni dai aka watse a taron.

Share.

game da Author