Da ‘yan Najeriya basu yafe wa Buhari ba, da bai zama shugaban kasa ba – Sheikh Gumi

0

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan mazaunin garin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa da ‘yan Najeriya basu yafe wa Buhari ba da bai zama shugaban kasa a Najeriya ba.

Gumi cikin fushi ya soki yadda ‘gwamnatin Buhari ke tozarta ‘yan Najeriya da sunan wai yaki da cin hanci da rasahawa.’

Gumi ya ce tuni mutanen kudu sun yi watsi da al’amuran gwamnatin Buhari kwata-kwata da irin salon mulkinsa a Najeriya.

” Mutanen kudu sun dade da fita daga al’amarin wannan gwamnati na Buhari, mutanen arewa ne kawai da basu san ciwon kan su ba.

Gumi ya kara da cewa idan Buhari na ganin shi mai gaskiya ne, ya zo a saka shi a mizani daya da tsohon shugaban kasa Shagari aga wanda yafi zama mara gaskiya.

Wannan zantuka sun fito ne daga bakin sheikh Gumi bayan ganin wani hotu da aka dauka na tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero a hukumar EFCC yana rike da kwali dauke da sunan sa da laifin da ake tuhumar sa da shi.

Share.

game da Author