Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar cewa ta tsinci gawar wata matan aure a cikin tsohuwar rijiya a karamar hukumar Birniwa a jihar.
Kakakin rundunar Audu Jinjiri wanda ya sanar da haka wa manema labarai inda ya bayyana cewa rundunar ta fantsama neman wannan mata ne mai suna Hadiza Adamu mai shekaru 30 bayan sanar wa yan sanda da ‘yan uwan ta suka yi cewa Hadiza ta bace tsawon kwanaki 20.
Jinjiri yace da suka fantsama neman Hadiza sai suka tsinci dankwalin ta a bakin wata tsohuwar rijiya dake kauyen Kazure a karamar hukumar Birniwa.
Ashe Hadiza ta fada cikin rijiyar ne. Sai dai yan sanda sun kama mijinta da suke yi wa zargin yana da masaniya kan bacewar matarsa.
‘yan sanda sun ce za a ci gaba da bincike don gano musabbabin aikata haka da Hadiza ta yi.