Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa ma’aikatar sa ta amince da a bude sabon sashe don kula da maganin gargajiya.
Ministan ya fadi haka ne a taton masana da aka yi a garin kano a makon da ya gabata.
Adewole ya ce tuni ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta amince musu da bude wannan sashe da zai kula da ayyukan magungunan gargajiyya.