Dalilin da ya sa zan yi takaran Sanata a Kano – Kawu Sumaila

0

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar majalisar tarayya, Hon. kawu Sumaila ya bayyana cewa ayyukan da yayi a tsawon shekarun sa a majalisar tarayya ne zasu haska shi a idanuwar jama’ar jihar Kano ta Kudu sannan ya sa har su zabe shi Sanata a 2019.

Hon Sumaila ya fadi haka ne a hira da yayi da PREMIUM TIMES a makon da ya gabata.

” Shekaru ta 12 a majalisar wakilai ta tarayya sannan kuma a cikin wadannan shekaru 8 daga ciki na yi su ne na a matsayin shugaba a majalisa.

” Kaga haka ya bani damar sanin duk wani abu da ake bukata a sani game da ayyukan majalisa.

” Sannan kuma irin ayyukan da na yi wa jama’a ta ma sun isa ace na samu nasara a wannan abu dana sa a gaba.

Da aka tambaye shi ko yana ganin zai iya kada sanatan da ke kan kujerar a yanzu, Hon Kawu ya ce tabbas yana da yakinin zai samu nasarar zama dan takarar sanata a Kano ta Kudu a Jam’iyyar APC.

Bayan haka Hon Sumaila ya kara yin bayani kan abin da ya ke nufi da cewa an yi ganganci wajen kin bin dokar jam’iyya a zaben dan takarar gwamna da aka yi a wancan lokaci.

Hon Sumaila ya ce ba kawai hakan da aka yi ya tsaya ga dan takarar gwamna ko na wani ofis da aka nema a siyasance bane, ya ce kuskuren da aka yi ya hada da wasu ofisoshin da akayi takara da ba a bi yadda dokar jam’iyya ta gindaya ba.

” Dalilin haka ya sa ba a sami yadda ake so ba yanzu duk da mun yi kokarin a gyara a wancan lokaci amma bai yiwu ba.

Share.

game da Author