Wasu mahara sun far wa shanun wani limamin cocin Angalika mai suna Benjamin Kwashe dake unguwan Kangan, karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Jos.
Maharan sun far wa Kanga ne da safiyar Asabar.
Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Terna Tyopev, ya sanar wa kamfanin dillancin labaran Najeriya, maharan sun kashe mai kula da shanun.
Sai dai mazaunan wannan unguwa sun shaida wa ‘yan sanda cewa suna zargin Fulani makiyaya ne da laifin aikata wannnan mummunar aika-aika.
Discussion about this post