TAMBAYA: Wanene mutumi na farko da ya fara musulunci bayan Annabi SAW?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Musulmin farko bayan Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wa Sallama, ita ce Nana Khadija Bintu Khuwailid, Allah ya yarda da ita, Matar Ma’aikin Allah, Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wa Sallama, ta farko. Dukkan malamai sunyi attifaki akan hakan.
Mutumin da ya riga kowa zuwa ga Musulunci bayan Nana Khadija, shi ne Mai gaskiyar wannan Al’uma Sayyadi Abubakar As-Sidiq, Allah ya yarda da shi, kuma manyan mutanen Makka sun shiga Musulunci ne ta Da’awar sa.
Wannan shi ne Ra’ayin Abdullahi Dan Abbas, Asma’ Bintu Abubakar, Imum Al-Nakha’i, Ibn Majushuni da sauran magabata da yawa.
A wata riwayar kuwa aka ce Sayyadi Aliyu Bin Abi Talib, Allah ya yarda da shi, shi ne farkon Musulmi bayan Nana Khadija Bintu Khuwailid, Allah ya yarda da ita. Musulunci ya zo Aliyu Allah ya yarda da shi yana yaro dan shekara goma, kuma yana zaune ne tare da Annabi Muhammad
Salallahu Alaihi wa Sallama. Wannan shi ne ra’ayin Salmanu Farisi, Abu Zarr, da Sa’idur Khudri da sauran magabata da dama.
A wata riwaya kuwa a kace Waraqatu Bin Naufar shi ne mutum na farkon Imani bayan Nana Khadija, wato masanin littafan Ahlul–kitabin nan da Khadija ta kai Annabi – Salallahu Alaihi wa Sallama- gurinsa bayan ya farfado daga firgicin ganin mala’ika a kogon Hira.
Waraqatu Bin Naufar ya tabbatar da annabcin manzo, kuma ya ce, zai taimaki Annabi a lokacin da mutanen sa za su fitar da shi da ga Makkah. Wannan kuma shi ne ra’ayin Imam Balkqini da wasu magabata.
A karshe malamai sun yi Ittifaqi cewa Nana Khadija ce ta farko a cikin mususlunci bayan shugaban halitta Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wa Sallama. Kuma sun yi sabani akan wane ne mutum na biyu bayan Annabi, inda Ibn Salah da Auza’i suka ce abinda ya dai-dai shi ne dunkule
ruwayoyin mabambanta da aiki da su kamar haka:
1. Abubakar Ibn Abi Quhafah -Allah ya yarda da shi- shi ne mutum nafakon Musulunta a cikin Maza.
2. Aliyu Bin Ibn Talib-Allah ya yarda da shi- shi ne mutum nafakon Musulunta a cikin yara.
3. Khadija Bintu Khuwaild-Allah ya yarda da ita- ita ce mutum nafakon Musulunta a cikin Mata.
4. Zaidu Ibn Sabit -Allah ya yarda da shi- shi ne mutum nafakon Musulunta a cikin ‘yantattun bayi.
5. Bilal Ibn Rabah-Allah ya yarda da shi- shi ne mutum nafako Musulunta a cikin bayi.
Allah shi ne mafi sani.