Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji daukar nauyin bai wa ‘yan bangar siyasa makamai.
Ya kuma tabbatar wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC cewa za a wadatar da jami’an tsaro da motocin zirga-zirgar su wajen yin sintiri a zaben 2019.
Idris ya kara da cewa, baya ga motocin sintiri, har da jirage helikwafta ‘yan sanda za su yi amfani su na sintiri a lokutan zaben 2019.
Idris ya bada wannan tabbaci ne a wani taron da INEC ta shirya kan tsare-tsaren zaben 2019 da batun kayan aikin zaben, a Legas jiya Alhamis.
Discussion about this post