Wasu magoya bayan Sanata Kabiru Marafa sun koka dangane da yadda aka hana su shiga Dandalin Eagle Square na Abuja, inda a yanzu haka ake ci gaba da taron jam’iyyar APC na kasa domin zaben shugabanni.
Cikin wata takardar manema labarai da suka aika wa PREMIUM TIMES, mai magana da yawun bangaren Marafa, Mohammed Bakyasuwa, ya bayyana cewa wasu wakilai na hakika daga jihar Zamfara ba su samu damar shiga dandalin taron ba, saboda kawai su na sanye da riguna masu dauke da hoton Sanata Kabiru Marafa.
Bakyasuwa ya ce su ne ‘yan APC na halak a jihar Zamfara, da ke karkashin zababben shugaban bangare daya na jam’iyyar, wato Surajo Gusau.
Da ya ke magana dangane da zaben da aka gudanar a jihar Zamfara, inda aka zabi shugabannin jam’iyya a bangarori biyu, Muhammed Bakyasuwa ya ce ai su bangaren Gwamna Abdul’aziz Yari ko fam ma ‘yan takarar sa ba su saya ba. Don haka ba za a kira su halastattu ba kena.
Daga nan ya sha alwashin daukar mataki dangane da abin da aka yi musu.