Tuggu, kutunguila, kumbiya-kumbiyar da aka kulla a zaben shugabannin APC

0

A daidai lokacin da ake ci gaba da fara zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa, wakilai masu jefa kuri’a daga kowace jiha, wato dalaget, sun rika samun takardu har guda uku mabambanta da juna, wadanda kowace ke kunshe da sunayen ‘yan takarar da ake so a zaba.

Takardar farko da aka fara raba wa masu zabe, ita ce mai dauke da jerin sunayen ‘yan takara 11, wadda aka yi zargin cewa an damka wa shugaban kwamitin shirya taron gangamin na kasa, Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar, kuma aka ce su ne ‘yan takarar da Shugaba Muhammadu Buhari ke so a zaba, wai su ne hankalin sa ya fi kwanciya da su.

Wata majiya, wadda ke daga cikin ‘yan takarar wani mukami a zaben ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Buhari ya fada wa Gwamna Badaru cewa ya tuntubi sauran ‘yan uwan sa gwamnoni domin su goyi bayan ‘yan takarar da ya ke so a zaba.

Wata majiya ta ce Buhari ya bayyana wa gwamnan cewa, wadancan su ne ‘yan takarar da ya ke so a zaba, su 11, amma a sauran mukamai, za su iya cikewa da wadanda ran su ke so.

A jerin sunayen da ke cikin takardar da ke dauke da ‘yan takarar da Buhari ke goyon baya, akwai Adams Oshimhole a matsayin shugaban jam’iyya, Faruk Aliyu a matsayin mataimakin shugaba daga Arewa, sai Mala Buni a matsayin sakataren jam’iyya na kasa.

Akwai kuma sunan Mainasara Sani a matsayinn wanda ake so a zaba mataimakin shugaban jam’iyya na shiyyar Arewa maso yamma, Emmanuel Eneukwu mataimaki daga shiyyar Kudu maso gabas, Hilliard Attah a matsayin mataimaki daga Kudu maso kudu, sai kuma Christopher Osuala a matsayin sakataren tsare-tsare na kasa.

Akwai kuma sunan Lanre Issa-Onilu a matsayin sakataren yada labarai na kasa, George Moghalu kuma mai binciken kudi na kasa, sai kuma Edike Adoh-Ogbuta a matsayin mataimakin lauyan jam’iyya.

Ita kuma Tina Adike, ita ce aka ce hankalin Buhari ya fi karkata ta zama shugabar mata ta kasa.

Akwai kuma wata takardar ta biyu da aka rika raba wa wakilan da za su yi zabe, wadda ita kuma aka ce su ne ‘yan takarar da jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ke so a zaba a matsayin shugabanni.

Shi dai wannan jerin sunayen, sun kunshi na ‘yan takara har 23.

Na farko akwai sunan Adams Oshimhole a matsayin shugaba, Niyi Adebayo a matsayin mataimakin shugaba daga kudu, Lawan Shu’aibu kuma mataimakin shugaba daga Arewa, Sai Kashim Imam a matsayin sakataren jam’iyya na kasa.

Amma daga baya Imam ya janye daga neman mukamin.

Akwai sunan Longers Anyanwu da ake so ya zama sakataren tsare-tsare na kasa, Salamatu Baiwa kuma shugabar mata ta kasa, da kuma Babatunde Ogala a matsayin lauyan jam’iyya.

Majiyar PREMIUM TIMES ta ce duk da alkawarin da gwamnoni suka yi wa Buhari ta hannun gwamna Badaru wanda shi ne shugaban shirya taro, cewa za a zabi wadanda Buhari din ke so a zaba, sai gwamnonin su ma suka fito da na su jerin sunayen da su ke so wakilan jefa kuri’a su zaba daga sama har kasa.

Shi dai wannan jerin sunaye da ke kunshe a cikinn takarda ta uku, ya kunshi sunayen ‘yan takara a mukamai daban-daban har 35.

Su ma sun amince da sunayen Adams Oshimhole, Faruk Adamu da Niyi Adebayo.

Sannan a na su jerin sunayen akwai Bulama Waziri, wanda ya rigaya ya janye wa Mai Mala Buni.

Akwai kuma sunan Fatima Adams a matsayin shugabar matan jam’iyya ta kasa, Bolaji Abdullahi a matsayin sakataren yada labarai na kasa da kuma Emma Ibediro a matsayin sakataren tsare-tsare na kasa.

Share.

game da Author