Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i na shirin komawa yajin aiki, saboda rashin cika alkawari daga gwamnati

0

Shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i, wadanda da ba malaman da ke koyarwa ba ne, sun bada sanarwar gudanar da taro na musamman a ranar 4 Ga Yuli mai zuwa, domin tattauna matakin da za su dauka, tunda Gwamnatin Tarayya ta ki cika musu alkawarin da ta dauka kafin su janye yajin aiki a watanni uku baya.

Idan ba a manta ba, kungiyar ta shiga yajin aiki ne a ranar 4 Ga Disamba, 2017, dangane da wani hakkin ta na naira biliyan 23.

Gwamnatin tarayya ta yi mata alkawari bayan watanni uku, amma har yau ba ta cika ba.

Sun janye yajin aikin ne a ranar 14 Ga Mayu, a bisa sharadin cika musu alkawari da gwamnati ta dauka.

Kungiyar dai a baya ta ba gwamnati wa’adin ta cika alkawarin da ta dauka a cikin makonni biyar, amma har yau ba ta cika ba, makonni 13 bayan daukar alkawarin.

PREMIUM TIMES a baya ta ruwaito inda gwamnati ta dauki alkawrin cewa za ta fara bayar da naira bilyan 8 a cikin makonni biyar domin a biya ma’aikatan a lokacin.

Ganin haka ne ya sa Kakakin Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i ta Kasa, Abdussobur Salaam ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa, ‘Gwamnatin Tarayya ta fadi ba nauyi, kuma ta ji kunyar rashin dattakon da ta nuna wa kungiyar su cewa ita ba gwamnati ba ce mai daukar alkawari ta na cikawa.”

Salaam ya ce wannan gwamnati sannan kuma ba ta bin umarnin kotu, domin babu ruwan ta da kotun ma. Y ace dukkan alkawurran da ta yi, da “kuma umarnin da kotu ta ba ta, babu wanda ta cika kuma babu wani ba’asin magana mai dadi ta kwantarwa ko sanyaya rayuka da zuciyar mu daga bangaren gwamnati.”

Salaam ya ci gaba da cewa ba za su yarda a yi musu bugu-biyu ba. “Da yawan mambobin mu da ke aiki a makarantun ‘ya’yan malamai da ma’aikatan jami’a sun rasa aikin su, kuma a yanzu haka Jami’ar Obafemi Awolowo na shirin korar wasu ma’aikatan.

“An zo ana yi mana wannan bi-ta-da-kulli a lokacin da aka yi mana alkawari aka ki cikawa, a lokacin da kotu ta bai wa gwamnatin tarayya umarni a kan mu, amma ta ki bin umarnin kotu, saboda ba gwamnati ba ce da ta san darajar cika alkawari da bin doka.”

Share.

game da Author