A ci gaba da wasan zagaye na farko na Gasar Cin Kofi Duniya da ke gudana a kasar Rasha, a yau ne Portugal ta yi nasara a kan kasar Morocco da ci daya mai ban-haushi.
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya jefa musu kwallo a raga a daidai minti na biyar da fara wasa.
Wannan ya kawo kasar Morocco ta zama ta biyu daga cikin kasahen Afrika da aka fara kwance wa zani a tsakiyar kasuwar kwallo, bayan da kasar Rasha ta fatattaki Eagypt jiya Talata.
Kungiyar Morocco ta yi bajinta sosai a wasan ta da Portugal, sai dai da ya ke Hausawa sun ce, ‘bukatar maje-Hajji Sallah’, Portugal ba ta samu nasarar jefa kwallo ba, duk kuwa da takurawar da ta yi wa Portugal bayan an dawo daga hutun rabi lokaci har aka tashi wasan.
A yanzu Ronaldo ne dai kan gaba da kwallaye 4. Wannan ya ba shi damar shiga gaban tsohon dan wasan kasar Hungary Ferens Puskas, mai yawan kwallaye 84 a tarihin gasar cin kofin duniya.
Ronaldo a yanzu ya na da kwallaye 85, hakan kuwa ya ba shi damar shiga gaban duk wani Bature a duniya da ya ci kwallaye a tarihin gasar.
A wasanni biyu da Ronaldo ya yi, ya ci kwallo da kafar dama, ya ci da ta hagu sannan a yau kuma ya ci kwallo da kai.
Discussion about this post