Alamomi na nuni da cewa jam’iyyar APC ta nemi duk wani wanda ke rike da mukami a yanzu kuma ya sake fitowa takara, da ya janye kafin ranar zabe kawai.
Majiya ta tabbatar da cewa wasu daga cikin shugabannin yanzu da ke kan tsayawa sabuwar takara, sun hada Mataimakin Shugaban Jam’iyya Shiyyar Arewa, Mai Mala Buni, Lawan Shu’aibu wanda shi ne Mataimakin Shugaba na Kasa.
Hilard Etta, daga Kudu maso Kudu, Emma Eneuku daga Kudu maso Gabas, sai kuma Sakataren Tsare-tsare, Osita Izunaso da kuma Bai Binciken Kudi na Kasa, George Muoghalu.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa duk wadancan sunayen an zubar da su daga cikin ‘yan takara, an bar suna Buni kawai daga cikin jerin ‘yan takarar, wadanda za a damka wa gwamnonin APC idan aka je wurin taro a yau Laraba.
Jerin sunayen amintattun ‘yan takarar dai su ne wadanda shugabannin jam’iyya suka fi so a zaba, duk kuwa da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a bar wadanda ke kai a yanzu su sake jaraba sa’a.
Sai dai kuma dukkan jiga-jigan APC da aka tuntuba, sun nuna cewa ba su san da wannan magana ba.
Da yawa kuma irinsu Abike Dabiri sun karyata cewa akwai wani jerin sunayen wasu shafaffu da mai da za a damka wa gwamnoni, da ake kira “Unity List.”
A ranar Asabar ne dai mai zuwa APC za ta yi taron gangamin ta a Abuja, inda za ta zabi sabbin shugabannin jam’iyyar.