YAJIN AIKIN JOHESU: Ma’aikatan asibitocin Kaduna sun bi sahu

0

Kungiyar ma’aikatan asibitocin gwamnati JOHESU reshen jihar Kaduna ta bi sahun sauraran jihohin kasar nan na shiga yajin aikin da uwar kungiyar ta kasa ta kira makonni biyar da suka wuce.

Idan ba a manta ba ana nan ana ta kai ruwa rana tsakanin kungiyar JOHESU da gwamnatin tarayya, inda ita kungiya ke neman lallai sai a inganta wa ma’aikatan asibiti albashi da sauran alawus-alawus kamar yadda likitoci ke morewa a kasar nan.

Hakan dai ya durkusar da ayyukan asibitocin kasar nan inda kullum kara tabarbarewa ya ke yi.

Gwamnati sun kasa gano bakin zaren.

A jihar Kaduna, kungiyar sun koka da halin ko in kula da gwamnatin jihar ke nuna wa ‘yan kungiyar.

Ta zargi gwamnati mai ci da yin watsi da karafe-Korafen su sannan kuma da kin mai da hankali wajen inganta asibitocin jihar da inganta albashi da alawus din ma’aikatan asibitocin jihar.

” Daga daren 18 ga watan Mayu, za mu bi sahun ‘yan uwan mu. Za a rufe asibitoci a fadin jihar, da na kananan hukumomi har sai gwamntai ta biya mana hakkokin mu. Mun ba ta isasshen lokaci amma ko waiwayar mu bata yi ba ballantana ta ce za ta taimaka mana.” Inji Ayuba Suleiman, Shugaban Kungiyar na jihar.

Share.

game da Author