YAJIN AIKIN JOHESU: Buhari, don Allah ka sa baki, mutane na mutuwa, Daga Aisha Yusufu

0

Yajin aikin da ma’aikatan asibitocin kasar nan karkashin kungiyar JOHESU suka shiga ya zama abin tashin hankali, fargaba da saka mutane cikin dimuwa da damuwa a kasar nan.

Abin da ke dada tada wa mutanen Najeriya hankali shine a kullum sai kaji maimakon ace an warware kullin ne, sai kara cikwuikuyewa al’amuran su ke yi ba a gaba ba a baya.

Abu dai kamar wasa, maganar ta na neman ta gagari gwamnatin Najeriya. Ministan Kiwon Lafiya ya kasa kulla wani abin azo agani, abin sai kara faskara ya ke yi.

Idan ba a gaggauta duba wannan matsala ba, toh fa allura zai hako garma, domin kuwa kusan dukkan asibitocin da ke kasar nan sun bi sahun ‘yan kungiyar. Idan ka tafi asibitocin kasar nan za ka ga a kulle suke.

Mutane na kokawa kan rashin maida hankali da gwamnati batayi ba na ganin an kawo karshen wannan yajin aiki.

Duk da cewa ‘yan kungiyar sun yi ta nanatawa cewa su ba so a maida su mataki daya da likitoci suke kira a yi musu ba, su ko likitoci tuni sun harzuka sun wasa takobinsu sun gwaggwalo idanu, suna ta hura hanci cewa kada gwamnati ta kuskura ta amsa kukan ma’aikatan asibitocin kasar nan.

Likitoci har barazana suka yi na idan har gwamnati ta yi amsa su, za su fara yajin aiki.

Anan mutane basu gane menene manufar likitoci ba. Duk da sune ke kan gaba da sauran ma’aikatan kiwon lafiyar da suma akwai kwararru da sauran masu kula da dakunan shan magani, jinya da sauran su, babu dalilin nuna wannan kiyayya ga kungiyar YOHESU din.

Yanzu dai da alamar abin ya fi karfin gwamnati da ministan Kiwon Lafiya, dole Buhari da kan sa ya gaggauta sa baki a wannan yajin aiki domin kuwa idan ba haka ba, za za a yi ta rasa rayukan marasa lafiya a kasarnan.

Kusan asibitoci a kananan hukumomi da jihohi, ma’aikatan asibitin ne ke taimakawa marasa lafiya, wasu harsu gama zaman su ba za su ga likita ba, karshen ta irin wadannan kwararru ne ke taimakawa har su sami sauki, gashi yau basu abin duk ya damalmale.

Buhari ka sa baki.

Share.

game da Author