Majalisar Wakilai ta yi fatali da kudirin da Honarabul Edward Pawjok ya mika gaban majalisar don ta zama doka da maza a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su za su dinga samun hutu idan matan su suka haihu.
‘Yan majalisa da suka tattauna batun a zauren ta sun ce wannan kudiri bai dace a kawo shi ma zauren majalisar ba.
Sun ce an san namiji da fita ne da nema wa iyalan sa. Babu wani dalilin da zai sa wai don matar sa ta haihu, kawai sai a wani bashi hutu.
Shi ko Pwajok, cewa yayi hakan zai sa maigida ya koma ga iyalan sa don taya mai dakin sa hidimar sabon jaririn da suka haifa.
Daga karshe dai gaba daya kaf majalisar sun ki amincewa da wannan kudiri inda nan take suka wancakalar ta ita.