Buhari zai iya zarcewa… Amma? Daga Hassan Ringim

0

Buhari dai asali ma bai yarda da tsarin mulkin farar hula ba, saboda zargin rashawa da karya doka.

Akan haka ya yi awon gaba da Shagari, ya yi gyara daidai gwargwado. Daga karshe abubuwa suka dagule. Daga bayane kuma wajejen shekarar 2001 ya lura mulkin na farar hula ya na da kyau, za a iya gyara kasa a ciki, har ya amince ya halarci wani taron siyasa na farko a gidan Mumbayya da ke Kano.

Buhari ya nemi takarar shugabancin kasa a shekarun 2003 a APP, 2007 a ANPP, 2011 a CPC, sai 2015 a APC. Kuma sai a na karshen ya kai labari, duk da ana zargin magudi akayi.

FAGEN SIYASA:

Kowa dai ya san maja da aka yi ce ta yi sanadin nasarar Buhari, bayan Tinubu ya jagoranci jahohin Yarbawa 6 su dangwalawa Buharin.

PDP ba shakka sun tsorata da yunkurin tsayawar takarar Buhari. Sai dai akwai abubuwan da za su iya sawa su ji sanyi;

Idan suka tsayar da dan takara daya mai kwari, wanda shi kadai zai buga da Buharin. Hakanan sai sun samu amincewar kungiyar da Obasanjo ya ke jagoranta, wana abu ne mai wahala.

APC za ta iya shiga rudani dangane da babban taronta, gami da tsayar da ‘yan takara. A karshe guguwar canjin sheka ta fantsama, kususan daga ‘yan majalissu.

Mutane kusan uku da suke neman takarar ba lallai sukai labari ba, idan duk sun tsaya. Misali;

-Idan Atiku ya tsaya takara, wanda da wuya ya samu a PDP sai dai ko wata haka, kamar SDP ko PDM.
– Idan Lamido ya samu takara a PDP.
– Idan shima Kwankwaso ya ce zai tsaya…

To kafin sha biyun rana, Buhari ya ci zabe.

Amma idan aka bar mutum daya kacal, kamar Kwankwaso ya ja layi a SDP ko PDP, to akwai alamun za a iya taron dangi a APC, ‘yan anti-party su taimaka, kujerar ta subulewa Buhari. Wanda ba lallai su Lamido da Atiku da wasun su, su yarda su barwa Kwankwaso ba.

KALUBALEN KASA:

Da farko dai kowa ya na zaton idan Buhari ya zama shugaban kasa, maganar rikici, fada, satar mutane da sauransu za su zama tarihi, sai dai abubuwa sun sauya;

Garkuwa da mutane ta ta’azzara a yankin Arewa, musamman Kaduna, zamfara da yankin Kudu(daman sun jima).

An kashe Fulani sosai da wasu Kabilu a Najeriya.

Boko Haram sun yi kokarinsu daidai gwargwado, don har wani abu aka yi mai kama da biki akan kwashe da dawo da daliban makarantar Dapchi.

Iyakokin Najeriya a bude suke ta bangaren shigo da makamai, musamman daga bangaren Arewa. Amma daga yankin gabar ruwa, kamar Lagos, custom sun yi kokari.

Rashin aikin yi ta’azzara sosai. Tsarin N-power da noman Shinkafa da Alkama ya samu matsaloli sosai.

Abincin da ake ciyar da dalibai abu ne mai kyau, sai dai akwai matsaloli. Bugu da kari y dace a fadada ciyarwar zuwa manya, saboda fama da yunwa da ake ciki.

Ba shakka masa’naantu ba su samu gatan da kulawar da ake bukata ba. A Kano da Lagos ba wani sabon abu da aka gani. Sai sai dalilin takaita hare-hare ga bututan mai, an samu daidaituwar tattalin arziki, da hauhawar asusun rarar mai a waje.

INKARI:

Dole ne Kowanne mai mulki ayi masa hakan a mulki. Sai dai Buhari na sa ya zo da salo. Misali;
√Sanin kowa ne duk wadanda EFCC ta ke kamawa da garkamewa, to ba a cikin APC ne. Sai dai abin nazarin shine, su Kansu wadanda suka taimaka aka ci mulkin da kudin gwamnati suka yi amfani da shi lokacin zabe.

A duk lokacin da mutane suka fara korafi akan halin da ake ciki, sai ggwamnati ta ce ai barnar da aka yi ba kadan ba ce. Bayan kuma don gyaran barnar aka zabesu, Kusan shekaru uku sai a hankali.

Wasu mutane da suka zagaye Buhari sun hanashi sakat. A lokacin da matarsa ta yi Bayani a BBC, da Naziru Mika’ilu ya tattauna da ita, ta nuna juya Buhari ake. Kuma mutane da ake zargi akwai Mamman Daura, Baba na Funtua, Abba Kyari, Lawal Daura da wasu a cikin jam’iyya kamar Tinubu.

Wata kila akan hakane, duk mukamai da kwangiloli suke zuwa da ayoyin tambayoyi.

KOKARI:

Ba shakka Buhari yayi kokari wajen rage satar kudin gwamnati, raunana Boko Haram, manyan ayyuka na tituna, da layin jirgin kasa, da gadoji da gidaje. Sai dai dukkansu akwai kalubale.

RUFEWA:

Abin da zan ce shine, Arewa baki dayanta ba ta da alkiblar komai, sai ta a hadu a saci kudi.
Akwai kungiyoyi masu yawa a Arewa, amma ba tsiyar da suka tsinana, kuma babu jjagora a cikinsu. Wata kila shi yasa ba wani babban aiki da gwamnati ta yi a Arewa. Hakan zai bayu ta ziyara ayyuka ko jaje zance, da ya kai a wasu yankuna a Arewa.

Maganar gaskiya Yarabawa ssu suka amfana da Buhari. Amma daman hakan bai zo da mamaki ba, don su suka yi sanadin zamansa. Domin kuwa mun yanda aka yi amfani da Shekarau a ANPP, da Ribadu a ACN don lalata nasarar Buhari a baya.

Mu Buhari na mu ne, don a Arewa yake. Amma akwai matsaloli da yawa na kasar nan da ke cikin kalubale, wasu ma ba a sanar da shi. Kuma bai isa ya nemi karin haske a kai ba.

Idan har ba wata matsala, idan muna so mu samu ci gaba mai tasiri, dole a samu wanda zai hau kujerar Buhari daga Arewa. Don ta hakane kadai za a gyara matsalolin bayan fage da ke damunmu.
Mu ne masu fama da fatara, talauci, Boko haram, yunwa, garkuwa da mutane, rashin aikin yi, bangar siyasa, rashin son juna, sai satar kudin kasa da ci da addini.

Share.

game da Author