Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Kasa Najeriya daga Kasar Amurka.
Buhari ya zayarci Amurka don amsa gayyatar shugaban Kasar Donald Trump.
A Amurka,shugaba Buhari ya tattauna da Trump kan yadda kasashen biyu zasu ci gaba da morar juna, musamman a fannonin bunkasa tattalin arziki, kasuwanci da cinikayya, tsaro da sauran su.
Shugaba Buhari ya kwashi buhunan yabo daga ‘yan Najeriya kan irin rawar da ya taka a kasar Amurka.
Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ba a barta a baya ba wajen luguden yabo da ake ta narka wa shugaba Buhari.
Ita ma ta jinjina wa mijin nata.
Discussion about this post