A karo na uku kenan Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris ya na gwasale Majalisar Dattawa, wajenn kin amsa kiran gayyatar da su ke yi masa, makonni uku a jere.
Majalisar na bukatar ya bayyana domin amsa wasu tambayoyi dangane da kama Sanata Dino Melaye da kuma kashe-kashe da ke faruwa a fadin kasar nan.
An fara gayyatar Idris ne a ranar 25 Ga Afrilu, 2018, amma bai je ba.
Sai dai a ranar da aka fara cewa ya bayyana ne, sai Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin ‘Yan sanda, Sanata Abu Ibrahim, ya bayyana wa Majalisa cewa Idris ya bayar da uzirin raka Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Bauchi, inda ya kai ziyarar kwana biyu.
A lokacin ne su ka sake rubuta wata sabuwar takardar gayyata, tare da kin amincewa mataimakin sa ya wakilce shi.
Sun sake gayyatar sa a ranar 2 Ga Mayu, 2018, amma bai halarta ba.
A wannan karo ne Sanata Abu Ibrahim ya ce bai samu jin ta bakin shugaban ‘yan sandan ba.
Ya ce daga baya ya samu labarin cewa ya je Kaduna ne, a maimakon amsa gayyatar da aka yi masa.
A wannan karo ne aka sake aika masa da gayyata a karo na uku, a bisa shawarar Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
An nemi ya bayanna a yau 9 Ga Mayu, 2018, amma har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labarin bai bayyana ba.
A lokacin da ya kamata a ce ya bayyana ya karato, majalisar ta fahinci cewa babu shi, kuma babu labarin sa.
Bayan an yi jira na dan takaitaccen lokaci ne sai Saraki ya bayyana cewa bai zo ba.
A zaman yanzu su na tattauna matakin da za su dauka a gaba.
Idan ba a manta ba, a ganawar da Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar da ya dawo a Abuja daga Daura, sun yi masa korafin yadda suka nemi Sufeto Janar din da ya bayyana a gaban majalisa har sau biyu, amma bai je ba.