Shugaban kungiyar gwamnonin matan Arewa kuma uwar gidan gwamnan jihar Bauchi Hadiza Abubakar ta bayyana cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare a yankin Arewa sannan ya lalata rayuwar matasan yankin da idan ba ayi wani abu cikin gaggawa akai ba za a fada cikin matsanancin hali a yankin.
Bayan haka Hadiza ta ce sun yanke shawara cewa kowace matan gwamna a kasar nan za ta bude wuri don horas da wadanda suka fada cikin wannan matsanancin hali da nufin ceto rayuwar su.
” Za kuma mu ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki na Arewa domin ganin mun kawo karshe wannan mummunar matsalar a yankin.”