Ma’aikatan jinya dake karkashin kungiyar JOHESU dake aiki a asibitocin jihohin kasar nan da kananan hukumomi sun bi sahu, suma sun fara yajin aiki.
Shugaban kungiyar na kasa Biobelemoye Josiah ya bayyana haka ne a yau Laraba inda ya ce ma’aikatan jinya na jihohi da kananan hukumomi duk za su bi sahu daga daren Laraba.
Ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan kin amincewa da bukatun su da gwamnati ta ki yi duk da zaman da ta yi da su.
” Dama mun fadi cewa hakan zai faru idan har dai gwamnati bata biya bukatun mu ba.”
A yanzu haka kungiyar ta na mako na hudu da fara wannan yajin aikin sannan marasa lafiya ne kadai yajin aikin ta fi shafa domin ko sun zo asibiti babu wanda zai taimaka musu da komai.