Akalla mutane takwas ne su ka mutu yayin da wasu tankoki biyu dauke da man fetur suka yi bindiga a garin Zing, cikin jihar Taraba.
An ruwaito cewa daya direban tankar ya na gudu ne domin ya tsere wa wasu sojoji da ke biye da shi domin su cim masa, sai motar ta kwace.
A wurin kokarin ya karkato motar ta koma kan titi ne, aka samu kuskure ya bangaji wata tanka wacce ita ma ta na tafita ne a kan titi.
Wani ganau ba jiyau ba, ya ce nan da nan sai wuta ta tashi, ta rika kama motocin da ke ajiye a gefen titi.
Hakan inji shi ya haddasa kowa ya tsere, inda garin gudu a kidime aka rika bakar juna, kowa na ta kan sa.
David Yohanna wanda ya tsere daga wutar, ya ce “sama da mutane 10 suka mutu nan take, kuma da dama sun ji raunuka.
“Har yanzu wutar ta can ta na ci, hayaki na tashi. Domin sai ma da muka yi amfani da bokitai muka rika watsa wa wutar, amma duk a banza.
Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, David Mosal, ya tabbatar da afkuwar hadarin.
Ya ce abin ya shafi mutane da yawa, saboda hadarin ya faru a ranar kasuwar garin ne.