Masarautar Dutse ta bada sanarwar tsige hakimi Bamaina Mustapha Lamido daga kujerar sarautar Kauyen.
Mustapha Lamido dai daya daga cikin ‘ya’yan tsohon gwamnan jihar Sule Lamido ne.
Sakataren masarautar Dutse, Amadu Malami ya sanar da haka sannan ya kara da cewa masarautar za ta nada sabon sarki a Bamaina nan ba da dadewa ba.
Masarautar ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin cewa shi wannan hakimi na Bamaina wato, Mustapha Lamido ya saka kan sa cikin harkar siyasa a jihar sannan kuma da badakalar handame wasu kudade da ake tuhumar sa da mahaifin sa sun handame lokacin da mahaifinsa ke mulkin jihar, cewa har yanzu gabadayan su na fuskantar tambayoyi daga hukumar EFCC.
Mahaifin sa, wato Sule Lamido, dai daya ne daga cikin ‘yan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP.