Hukumar Jin Dadin Alhazai na babban birnin tarayya, Abuja ta sanar cewa hukumar za ta fara yi wa maniyyata tambihi kan hajji daga ranar 2 ga watan Mayu.
Kakakin hukumar Muhammad Aliyu ne ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba.
Ya ce malaman da za su koyar da maniyyata sun fara hallara sansanin hajji dake Abuja.
Ya kuma kara da cewa bana sun kasa darussan koyar da maniyyatan zuwa kashi hudu domin inganta aikin tambihin.
” Za a koyar da darussan da suka hada da wayar da maniyyata yadda za su yi aikin hajji gaba daya da wayar musu da kai game da sabbin dokokin da kasar Saudiyya suka fitar da kuma na hukumar Alhazai na kasa.
A karshe ya yi kira ga maniyyatan da su yi mafani da wannan dama matuka.
Discussion about this post