Mutanen garin Maiduguri na murna da shirin rusa matattarar karuwai da mashaya muggan kwayoyi

0

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta dauko ra’ayoyin wasu mazaunan garin Maiduguri jihar Barno game da shirin kora da rusa gidajen karuwai da wuraren da ake sha da siyar da miyagun kwayoyi a jihar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Barno ta ba mazauna unguwan Galadima dake Maduguri wa’adin kwanaki 14 da su tattara nasu-inasu su kauce daga wannan unguwa cewa duk rusa su za ayi.

Galadima na daya daga cikin unguwannin da ke cikin garin Maiduguri da nan ne mafakan karuwai da inda a ke harkar miyagun kwayoyi da duk abubuwan ta’asa.

Gwamnatin jihar Barno na kokarin yi wa kanta rigakafi ne tun da wuri, saboda a ire-iren wadannan wurare ne Boko Haram kan boye da kuma wasu ‘yan ta’adda da batagari.

Wani mazaunin garin Maduguri mai suna Ibrahim Bashir ya jinjina wa gwamnati kan tadawa da kuma rusa wannan unguwa cewa barin sa gurgunta ci gaban jihar yake yi.

Shima Said Danna yace yana goyan bayan rusa wannan unguwa.

Shi kuwa Ali Bukar dake zama a Baga cewa yayi tada su da rusa wannan unguwa ba zai yi maganin ta’addancin ba. Ya ce shiri ne za a kirkiro domin seta halayyar wadanna karuwai da matasa ba rusa unguwar ba.

Abubakar Suleiman a nashi tsokacin ya ce tada su ba tare da an samar musu da abin yi ba kwanto kura ce za ayi a jihar idan suka bazu. Yace a kirkiro shirye-shirye domin inganta rayuwar su da kuma sama musu madafa.

Abdulhameed Bukar dake zama a unguwan Jere ya ce rusa unguwa daya kawai bai isa ba, domin akwai wasu mugan unguwanni kamar Gamboru, Moduganari, Wulari, Hot Bite, Baga Road, Mairi, London Ciki, Artillery da Mami markets din dake cikin barikin sojoji, duk ya kamata a tada su idan tsaftace garin a ke so ayi.

Share.

game da Author