Ma’aikatan lafiya za su janye yajin aiki – Inji shugaban JOHESU

0

Hadaddiyar kungiyar ma’aikatan asibitocin Najeriya da ma’aikatan jinya karkashin inuwar JOHESU sun ce suna tattaunawa a tsakanin su domin komawa aiki kamar yadda kotu ta umurce su da suyi.

Mataimakin shugaban kungiyar Ogbonna Chimela ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa lallai kungiyarna ganawa a tsakanin mambobin ta domin janye yajin aikin.

Ogbonna Chimela, ya bayyana cewa tabbas akwai maganan yiwuwar janye yajin aikin kwananan sai dai basu tsayar da rana ko lokaci ba tukunna.

” Muna tattaunawa a tsakanin mu, domin yadda za mu fuskanci abin. Wato yadda zamu roki mabiyan mu da kuma tsayar da rana domin janye yajin aiki. Abin da muke so ku sani shine kotu ta yanke hukunci akai saboda haka zamu duba mu ga komai anyi shi ciki fahimta tunda akwai hukuncin kotu akai.

Idan ba a manta ba, kungiyar JOHESU sun fara yajin aiki bayan jin amincewa da a biay musu bukatun su da suka mika wa gwamnati.

Kwanaki sama da 40 kenan asibitocin kasar nan na fama da rashin maiakatan kiwon lafiya a asibitocin.

Share.

game da Author